Zaben 2019: Dalilin da ya sa na zabi Getso a matsayin abokiyar takarata - Moghalu
- Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar YPP, Farfesa Kingsley Moghalu, ya kaddamar da yakin zabensa da sakin littafinsa mai suna BIG (Build, Innovate, Grow)
- Moghalu ya ce littafin wani kundi ne na kyawawan manufofi wanda hatta magadansa zasu iya dorawa akansa, kuma, kowanne dan Nigeria na da kyakkyawar makoma
- Dangane da zabar Umma Getso a matayin abokiyar takararsa, Moghalu ya ce, babu wanda zai fi fahimtar kasar kamar mata. Kuma babban kuskure ne mayar dasu saniyar ware
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Young Progressives Party (YPP), Farfesa Kingsley Moghalu, ya kaddamar da yakin zabensa da sakin littafinsa a yanar gizo da za a iya saukewa kyauta, mai suna BIG (Build, Innovate, Grow), wanda a cikinsa ya bayyana manufofi da kuma kudorinsa ga Nigeria a 2019.
"Cikin nustuwa na rubuta dukkanin kudurorina da manufofina a cikin wannan littafin nawa, zan iya cewa, nine dan takarar shugaban kasa na farko da ya fara yin hakan. Ba wai wani kundi bane na tsare tsare ko kuma kawai shiri na 'yan shekaru, a'a, wani kundi ne na kyawawan manufofi wanda hatta magadana zasu iya dorawa akansa, da wannan littafin nawa na BIG, kowanne dan Nigeria na da kyakkyawan yakini da makoma daga shekarar 2019" a cewar Moghalu.
A cikin wata sanarwa da aka samarwa manema labarai a Legas, dan takarar shugaban kasar ya kuma bayyana dalilin da ya sanyashi zabar 'yar shekaru 71, Mrs. Umma Getso a matsayin abokiyar takararsa a zaben 2019.
KARANTA WANNAN: Dama can APC bata yiwa 'yan Nigeria alkawarin gyara kasar a cikin shekaru 4 ba - Fashola

Asali: Depositphotos
"Na zabeta saboda an sha sanar dani cewa zabar mace a matsayin abokiyar takara baban kuskure ne. An shawarce ni akan kada nayi hakan, saboda babu ta hanyar da mace zata taimaka wajen samun nasarar zabe idan anzo kada kuri'a.
"Sai dai ni kuma hakan nake so. Mun dade muna gudanar da kasa, inda za a ce karka yi kaza, saboda kaza ba zai samar da nasara ba; kuma wannan ne dalilin da ya sa har yau babu wani ci gaba a mulkin fararen hula tun 1999.
"Mata suna daga cikin masu gina kasa. Sune iyayenmu, kannai da yayyen mu, 'yan uwanmu, abokanmu, matanmu, masu karfafa mana guiwa, da dai sauransu. Babu wanda zai fi fahimtar kasar nan kamar mata. Babban kuskure ne yadda aka mayar dasu saniyar ware a fagen siyasa tsawon shekarun nan," a cewar sa.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng