Biyu-babu-wanwar: Diyar David Mark ta fice daga jam'iyyar PDP, ta kuma tona mata asiri
Daya daga cikin 'ya'yan tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Blessing Onuh ta sanar da ficewar ta daga jam'iyyar mahaifin ta Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA).
Blessing Onuh, wadda bayan sauya shekarar ta ta ta kuma samu tikitin yin takarar kujerar 'yar majalisar mazabar Otukpo/Ohimini a majalisar wakilai, ta bayyana tsohuwar jam'iyyar ta ta da cewa ba ta da adalci.

Asali: UGC
KU KARANTA: Rahama Sadau ta bayyana wanda zata zaba a 2019
Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa diyar ta David Mark jim kadan bayan ta sauya shekar tare da dumbin magoya bayan ta da suka kai mutane dubu 15, ta kuma kai ziyarar ban girma ga dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar a zaben 2019.
A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya a ranar Litinin din da ta gabata ta gurfanar da wasu mutane uku a gaban kotun tarayya dake zaman ta a garin Legas bisa laifin damfarar mutane da sunan shugaban kasa, Muhammadu Buhari da matar sa, Aisha Buhari.
Majiyar mu ta ruwaito cewa mutanen da ake zargi da suka hada da Uche Anyanwu Julius, da ke anfani da Musa Mohammed; Kenneth Chikwado Ezeomu, da ke anfani da Abdul Karim; da Agu Ifeanyi George, da ake kira Dakta Lina Norman sun damfari jama'a da dama.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng