Yanzu Yanzu: Yan sanda da mutanen unguwa sun dakile wani fashin banki a Ile-Ife

Yanzu Yanzu: Yan sanda da mutanen unguwa sun dakile wani fashin banki a Ile-Ife

Yan unguwa sun dakile wani hari da wasu yan fashi suka yi yunkurin kai wa wasu bankuna a yankin Lagere da ke Ile-Ife, jihar Osun a ranar Litinin, 19 ga watan Nuwamba.

Bakunan ciniki bakwai ne ke yankin Lagere sannan kuma yan fashin sun isa yankin da misalin karfe 10 na safe.

A cewar wasu idanun shaida, yan fashin wanda suka kai mamaya yankin a wata motar Camry da wata bus, suka paka kusa da wani bankin ciniki a yankin sannan suna ta harbi a sama don tsoratar da mutane.

Yanzu Yanzu: Yan sanda da mutanen unguwa sun dakile wani fashin banki a Ile-Ife
Yanzu Yanzu: Yan sanda da mutanen unguwa sun dakile wani fashin banki a Ile-Ife
Asali: Depositphotos

Don haka, jami’an yan sanda na bankunan da mambobin kungiyar yan banga a yanki suka far ma yan ta’addan da karfi.

KU KARANTA KUMA: Buhari, Obasanjo, Atiku za su hade wajen kaddamar da littafin Jonathan a gobe

Da aka kira don jin ta jin bakin hukumar yan sanda, kakakin yan sandan Osun Odoro (SP), ya tabbatar da lamarin ya kuma ce yan sanda na nan suna bin sahun yan fashin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng