Dandalin Kannywood: Rahama Sadau ta bayyana wanda zata zaba a zaben 2019

Dandalin Kannywood: Rahama Sadau ta bayyana wanda zata zaba a zaben 2019

- Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood ta goyi bayan kiran da wani mutum ya yi cewa 'yan Najeriya su zabi mutum na gari a 2019 a kowacce jam'iyya yake.

- Jarumar ta bayyana haka ne a cikin amsar da ta bai wa masu bibiyar shafinta na Twitter.

Legit.ng Hausa ta samu cewa jarumar da farko tayi tambaya ne a game da hakan a shafin ta na dandalin sadarwar zamani na Tuwita inda ta tambayi mabiyan ta ko 'wanne dan takara za su zaba a zaben na 2019.

Masu bibiyarta sun bayar da amsoshi daban-daban, amma da alama amsar da ta fi burge jarumar ita ce wadda wani mai suna A.B Danbatta ya bayar.

Dandalin Kannywood: Rahama Sadau ta bayyana wanda zata zaba a zaben 2019
Dandalin Kannywood: Rahama Sadau ta bayyana wanda zata zaba a zaben 2019
Asali: UGC

KU KARANTA: An samu sabuwar jaruma a masana'antar Kannywood

"Kowanne mutum shi zai yanke hukunci kan shugaban kasar da zai zaba na gaba, babu wanda zai yanke maka wannan hukuncin sai kai da kanka. Amma ina bayar da shawara ga dukkan 'yan Najeriya su zabi mutum na gari ko daga wacce jam'iyya yake."

Daga nan ne Rahama Sadau ta nuna gamsuwar ta inda ta ce "Wannan ita ce amsar da nake so a ba ni Allah ya yi maka albarka

Da dama dai daga cikin takwarorin jarumar na Kannywood sun fito fili sun bayyana dan takarar da za su goya wa baya ba a zaben 2019.

Yayin da jarumai irinsu Adam A. Zango da Fati Shu'uma da makamantansu suka bayyana goyon bayansu ga Shugaba Muhammadu Buhari su kuma jarumai irinsu Sani Danja da Fati Mohammed da Maryam Booth sauransu sun ce tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar za su zaba a 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel