Hassada ce: Wani masoyin Kwankwaso ya mayarwa da Buhari raddi game da kalaman sa
Wani masoyin Sanata Kwankwaso, Mustapha Abdullahi Inuwa Jauben Gadanya, Kano yayi wa shugaba Buhari wankin babban bargo musamman ma game da kalaman sa akan jagoran na su da yayi a kasar Faransa da yace ya karkatar da kudaden jihar zuwa yin kamfe din sa.
Mustapaha Abdullahi dai ya bayyana cewa abinda shugaban kasa ya fada akan Dr Rabiu Kwankwaso ba gaskiya bane, kowa ya san hassada ce yake masa saboda Allah ya daukaka Kwankwaso kuma ya ba shi farin jinin al'umma.

Asali: UGC
KU KARANTA: Karin albashi: Gwamnoni sun ce za su rage ma'aikata
Legit.ng Hausa ta samu cewa Kwankwaso ya shiga garin Kano din a wani yanayi na bazata kuma irin ta ta farko tun bayan saukar sa daga mulki a shekarar 2015.
A wani labarin kuma, Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun sanar da samun nasarar cafke wasu gawutattun matsafa masu suna Tochukwu Udoye da John Paul a unguwar Odoguyan, karamar hukumar Ikorodu, jihar Legas.
Haka zalika 'yan sandan sun bayyana cewa matsafan da suka kama mambobin kungiyar matsafa ta Aye ne kuma sun kama su ne suna kokarin kashe wani mazaunin jihar Ridwan Kosamotu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng