Masana tsaro, malamai da Sarakuna a Najeriya na wani muhimmin taro kan 'yan Boko Haram
Masana da kwararru kan harkokin tsaro a ciki da wajen Najeriya, malamai da kuma sarakunan gargajiya yanzu haka suna gudanar da taron wuni uku kan matsalar yakin sunkuru na mayakan Boko Haram a Najeriya.
Taron dai kamar yadda muka samu, cibiyar wayar da kan jama’a da al’amuran addinin musulunci da tattaunawa tsakanin mabiya addinai ta Jami’ar Bayero Kano da hadin gwuiwa da gwamnatin tarayya da jihar Kano ne suka shirya taron.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Maciji ya makalewa wani a baki yayin da yake wasa da shi
Legit.ng ta samu cewa a wurin taron, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya alakanta tattalin arziki da zaman lafiya da kuma fatara da talauci a matsayin abubuwan da ke kara ruruta wutar rikicin.
A wani labarin kuma, Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun sanar da samun nasarar cafke wasu gawutattun matsafa masu suna Tochukwu Udoye da John Paul a unguwar Odoguyan, karamar hukumar Ikorodu, jihar Legas.
Haka zalika 'yan sandan sun bayyana cewa matsafan da suka kama mambobin kungiyar matsafa ta Aye ne kuma sun kama su ne suna kokarin kashe wani mazaunin jihar Ridwan Kosamotu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng