Karin albashi: Gwamnoni sun ce a saurari rage yawan ma'aikata

Karin albashi: Gwamnoni sun ce a saurari rage yawan ma'aikata

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta bayyana cewa idan dai har aka dage kan lallai-lallai sai sun biya karin mafi karancin albashi na Naira dubu 30, to fa gaskiya sai dai su rage yawan ma'aikatan su.

Shugaban gwamnonin na Najeriya Abdul Aziz Yari dake zaman gwamnan jihar Zamfara ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala wani zaman gaggawa da gwamnonin suka gudanar a jiya, garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Karin albashi: Gwamnoni sun ce a saurari rage yawan ma'aikata
Karin albashi: Gwamnoni sun ce a saurari rage yawan ma'aikata
Asali: Facebook

KU KARANTA: Rundunar sojin ruwan Najeriya ta kaddamar da yakin sunkuru

Legit.ng Hausa ta samu cewa gwamnan ya kara da cewa Naira dubu 30 tayi masu yawa kuma ba su iya biyan ta domin a lissafin da suka yi ma, jihar Legas ce kadan zata iya biyan hakan ita ma don tana samun kudaden shiga da yawa ne ta hanyoyi daban.

Daga nan ne kuma ya ce tuni kungiyar sa ta nada wani kwamiti na musamman da zai gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a kan batun domin samun matsaya da kowa zai yi na'am da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng