Babbar asara: Wata mota mai dauke da kayan N500m ta kone kurmus a Kebbi

Babbar asara: Wata mota mai dauke da kayan N500m ta kone kurmus a Kebbi

- Wata babbar mota mai dauke da kayayyakin N500m kan hanyarta ta zuwa Birnin Kebbi, ta kama da wuta bayan da ta ci karo da wata wayar wutar lantarki a kan wata babbar hanya

- Wani da hatsarin ya afku a gaban idonsa, Alhaji Adamu Tanko, ya ce motar ta kone kurmus, sai dai direban da kuma karoan motar sun tsallake rijiya ta baya-bayan

- Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda ta jihar Kebbi, DSP Danjuma Possy, ya ce, lamarin ya faru ne kan hanyar Jega zuwa Birnin Kebbi da karfe 11am

A ranar Laraba, wata babbar mota mai dauke da kayayyakin N500m da ta fito daga kasuwanni daban-daban, a kan hanyar ta ta zuwa Birnin Kebbi, ta kama da wuta bayan da ta ci karo da wata wayar wutar lantarki a kan wata babbar hanya.

Wani da hatsarin ya afku a gaban idonsa, Alhaji Adamu Tanko, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Birnin Kebbi, cewar motar ta tsinke wayar wutar, wacce ta haddasa tashin tartsatsin wuta, da ya yi sanadin kamar motar da wuta.

Tanko ya ce motar ta kone kurmus, sai dai direban da kuma karoan motar sun tsallake rijiya ta baya-bayan, bayan sun samu nasarar ficewa daga cikin motar.

KARANTA WANNAN: Iftila'i ya fada jahar Kano: Gobara ta lamushe wani gini da shago Rijiyar Zaki

Babbar asara: Wata mota mai dauke da kayan N500m ta kone kurmus a Kebbi
Babbar asara: Wata mota mai dauke da kayan N500m ta kone kurmus a Kebbi
Asali: Depositphotos

Wanda amarin ya faru a gabansa mutanen da ke wajen sun kira hukumar kwana kwana, wacce ta iso cikin gagawa tare da ceto wasu kaya 'yan kadan da suka rage basu ci wutar ba.

Kayayyakin da motar ke dauke da su sun hada da kekuna, atamfofi da shaddoji, kayan wutar lantarki, tayils, fankoki, injinin samar da wutar lantarki, kayan abinci, bakin mai, man gyada da dai sauransu, mallaki sama da 'yan kasuwa 100 daga kasuwanni daban-daban a Birnin-Kebbi.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda ta jihar Kebbi, DSP Danjuma Possy, ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa, lamarin ya faru ne kan hanar Jega zuwa Birnin Kebbi da misalin karfe 11 na safiyar Laraba, 14 ga watan Nuwamba, sai dai ba a yi asarar rayuka ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng