Lafiya uwar jiki: Hanyoyi 6 na kare kai daga kamuwa da cutar suga
Ciwon suga ko diabetes ciwo ne da kan kasance tare da mai fama da shi na tsawon rayuwa wanda kuma kan yi sanadin mutuwar fiye da mutum miliyan daya a kowace shekara - kana kowa na iya kamuwa da shi.
Ciwon na da dangantaka mai karfi ta wajen gado da yanayin da mutum ya sami kansa, amma mutum na iya rage yawan sugar da ke cikin jinin jikinsa ta hanyar kula da irin abincin da yake ci da yawan yadda yake motsa jikinsa.

Asali: UGC
KU KARANTA: Kungiyoyin kwadago sun ba Buhari dama ta karshe kan karin albashi
Ga dai wasu hanyoyi nan da ka iya kare mutum daga kamuwa da ciwon:
1. Rage cin abinci mai sukari sosai
2. Yawan ci ko kuma shan kayan marmari
3. Rage cin ababen da aka yi da fulawa kamar farin biredi da taliya. A madadin haka sai ya ci wadanda aka yi da alkama.
4. Yana da muhimmanci mutum ya daina cin abincin da zarar ya ji ya koshi.
5. Motsa jiki na taimakawa wajen rage bugun jinin jiki da rage yawan suga a jikin dan Adam
6. Yana kuma da muhimmanci mutum ya guji shan taba kuma ya rage cin abinci mai maiko.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng