Zaben 2019: Musulman Filato sun mika wata muhimmiyar bukatar su ga gwamnan jihar
Bayan yadda aka yi ta magabganu a kafofin yada labarai a cikin farkon satin nan game da zabin mace kuma musulma da gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-rufai yayi a matsayin mataimakiya a zaben shekarar 2019, suma musulmai a jihar Filato sunyi magana.
Mutane da dama ke ganin tamkar gwamnan bai kyauta ba musamman ma ganin yadda jihar ke fama da rikici da ke da alaka da addini da kanilanci, wasu kuma sun kafa hujja ne da jahohi irin su Filato inda sukace ba'a baiwa musulmai mukamin mataimaki duk kuwa da yawan su.

Asali: UGC
KU KARANTA: Wani bature ya musulunta bayan karanta Al-qur'ani
Legit.ng Hausa ta samu cewa wannan ne ma ya sa al'ummar musulmai daga jihar ta Filato kamar wani Lauya mai suna Lawal Ishaq ya bayyana cewa suma a ko don yawan su a jihar da yace yakai kusan kaso 40 cikin dari, ya kamata a basu mukamin mataimaki a zaben 2019 mai zuwa.
Babban lauyan ya kara da cewa kananan hukumomi kamar Wase da Jos ta Yamma musulmai ne suka fi yawa, haka nan kuma a kananan hukumomin Mngu, Quan’pan, Shendam, Bassa, Barkin Ladi da Jos ta Kudu duk akwai musulmai da yawan gaske.
A wani labarin kuma, kungiyoyin kwadago a Najeriya sun baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari daga nan zuwa watan DIsemba a matsayin dama ta karshe gare shi da ya tabbatar da dabbaka karin albashi.
Haka zalika kungiyoyin sun kuma bayyana cewa idan ya kuskura ya rage kudin mafi karancin albashin daga Naira dubu 30, to tabbas za su hargitsa gwamnatin komai ya tsaya cak don su ba wasa suka zo ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng