Biyu babu: Shekaru yayi magana game da kishin-kishin din cire sunan sa a takarar Sanata

Biyu babu: Shekaru yayi magana game da kishin-kishin din cire sunan sa a takarar Sanata

Tsohon gwamnan Kano kuma daya daga cikin jiga-jigan siyasar Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau yayi magana game da kishin-kishin din da ke yawo kan batun cire sunan sa daga cikin masu takarar kujerar Sanata a jihar Kano a zaben 2019.

Tsohon gwamnan wanda kuma yanzu jigo ne a jam'iyya mai mulki ta APC ya yi magana ne kan batun a ta bakin mai magana da yawun sa, Malam Ghali Sadiq wanda yace zancen ba gaskiya bane, labarin kanzon kurege ne kawai.

Biyu babu: Shekaru yayi magana game da kishin-kishin din cire sunan sa a takarar Sanata
Biyu babu: Shekaru yayi magana game da kishin-kishin din cire sunan sa a takarar Sanata
Asali: UGC

KU KARANTA: An binciki Atiku bayan dawowa daga Dubai

Legit.ng Hausa ta samu cewa a baya an fara yawo da maganar cewa jam'iyyar APC a jihar ta Kano tana shirya kullaliya ta karkashin kasa na canza sunan tsohon gwamnan da wani dan takarar na daban.

A wani labarin kuma, Sanata Enyinnaya Abaribe dake zaman wanda ya tsayawa hatsabibin nan Nnamdi Kanu aka bayar da shi beli a shekarar da ta gabata ya shiga tsomomuwa bayan da shi Nnamdi Kanu din ya sulale ya bar kasar nan a shekarar da ta gabata.

Mun samu cewa tuni ma dai Sanatan ya umurci Lauyan sa da ya rubutawa kasar Isra'ila inda aka ga hotunan Nnamdi Kanu din sun bulla da su bashi cikakkun bayanai game da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel