PDP za ta fatattaki APC daga Aso Rock a 2019 – Kungiyar Atiku
Kungiyar kamfen na dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, sun bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki za ta sha kaye a zaben 2019.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa shugaban kungiyar Atiku: : Change the Change for Progress, Ken Nwadinobi, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 11 ga watan Nuwamba a wajen kaddamar da kungiyar kamfen na PDP reshen jihar Katsina.
Legit.ng ta tattaro cewa Nwadinobi ya bukaci mutanen jihar da Najeriya da kada su ji kowani tsoro akan Atiku, cewa zai yi masu shugabanci nagartacce da kuma kare yancinsu.

Asali: Depositphotos
Ya bayyana cewa saboda wannan dalili ya kamata dukkanin yan Najeriya su zabi Atiku a matsayin shugaban kasa, inda yace kasancewar Katsina garin Atiku na biyu za su amfana sosai domin cewa zai ci gaba ne kan sahun marigayi tsohon shugaban kasa Umar Musa Yar’Adua wanda ya kasance dan Katsina.
KU KARANTA KUMA: 2019: Tsohuwar shugabar EFCC Waziri ta gargadi yan siyasa akan rikici da kalaman kiyayya
A nashi bangaren Muttaqa Rabe Darma yace gwamnatin APC ta gaza magance matsalar tsaro, sace-sacen mutane da kuma fashi da makami.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng