Musulunci ya samu karuwa: Peter da Joshua sun koma Muhammad da Sulaiman a birnin Jalingo

Musulunci ya samu karuwa: Peter da Joshua sun koma Muhammad da Sulaiman a birnin Jalingo

Wasu bayin Allah sun samu shiga addinin musulunci a ranar Juma'a bayan kammala sallar Juma'a a masallacin Bin Fodio dake birnin Jalingo, inda shugaban Majalisar Malamai na kasa na Kungiyar Izala Dr Ibrahim Jalo Jalingo ke limanci.

Wanda kuke gani da kananan kaya kafin ya musulunta sunansa Joshua yanzu kuma ya dawo Sulaiman.

Musulunci ya samu karuwa: Peter da Joshua sun koma Muhammad da Sulaiman a birnin Jalingo

Musulunci ya samu karuwa: Peter da Joshua sun koma Muhammad da Sulaiman a birnin Jalingo
Source: Facebook

Wanda yake sanye da jamfa kafin ya musulunta sunansa Peter, yanzu kuma ya dawo Muhammad.

Muna rokon Allah (T) Ya tabbatar dasu a cikin musulunci.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kaduna kuma daya daga cikin jiga-jigan jam'iyya mai mulki ta APC, Malam Nasir El-rufai yayi wa jam'iyyar PDP kaca-kaca inda ya ce ba sauran mai tunani da ya rage a jam'iyyar yanzu.

Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a yayin da yake maida martani ga jam'iyyar ta PDP da a farko ta caccake shi biyo bayan kalaman gwamnan inda ya aibata tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi dake zaman mataimaki ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel