Hukumar SSS ta kama masu garkuwa da mutane da yan kungiyar asiri 17

Hukumar SSS ta kama masu garkuwa da mutane da yan kungiyar asiri 17

Hukumar yan sandan farin kaya(SSS) sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da garkuwa da mutane da kuma yan kungiyar asiri a wasu jihohin kasar da suka hada da Kaduna da Katsina.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Peter Afunanya ya bayyana a waa sanarwa a Abuja a ranar Alhamis, 8 ga watan Nuwamba cewa an kama biyar daga cikinsu a ranar 25 ga watan Oktoba a Riga Chikun, jihar Kaduna.

Mista Afunanya ya bayar da sunayensu a matsayin Ahmadu (shugaban kungiyar), Suleiman Umar (mai tattauna kudin fansa), Ibrahim Mallam, Ishaku Saidu wanda aka fi sani da Ishe da kuma Mansur (Mallam).

Hukumar SSS ta kama masu garkuwa da mutane da yan kungiyar asiri 17

Hukumar SSS ta kama masu garkuwa da mutane da yan kungiyar asiri 17
Source: Depositphotos

Yace bayan binciken farko, an gano mabuyar kungiyar a jihar Katsina inda aka yi nasarar kama wasu biyu, Muhammadu Ibrahim da kuma Muhammed Isa.

Yace da farko a ranar 19 ga watan Oktoba an kama wani mai garkuwa da mutane Sirajo Ibrahim a Hayim Danmni, karamar hukumar Igabi da ke Kaduna..

Jami’in hulda da jama’a yace an kama wasu biyu Abubakar Umar da Suleiman Sani bisa zargin safarar bindiga.

Mista Afunanya yace an kama masu laifin a ranar 30 ga watan Oktoba a Sainyinan, karamar hukumar Yabo da ke jihar Sokoto.

KU KARANTA KUMA: Mafi karancin albashi: Kaso 95 bisa 100 na gwamnonin kasar nan ba za su iya biya ba – Gwamna Umahi

An kuma kama wasu yan fashi Dan-Alhaji, Dan-Mineri,Yusuf Khalif da Musa (Mallam) a kusa da jihar Zamfara.

An sake kama Muhammed Aminu, da Dare Okunwola, wanda aka fi sani da boda.

Hakazalika an kama wasu yan kungiyar asiri Yakubu Mohammed da Joseph Andoaasin a jihar Benue.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel