Nigeria ce ta 2 a duniya wajen yin kashi a bainar jama'a - Buhari

Nigeria ce ta 2 a duniya wajen yin kashi a bainar jama'a - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa kan yadda kasar ta zamo na 2 a duniya wajen yin kashi a bainar jama'a

- Buhari ya ce kaddamar da dokar ta bacin ya zama wajibi ne don rage yawaitar cututtukan da ake kamuwa dasu daga ruwa maras tsafta da kuma kazantar muhalli a fadin kasar

- Ya ce samuwar bututun raba ruwa ya kai kashi 32 a 1990 amma ya ko,a kashi 7 a 2015; samar da tsaftataccen muhalli ya ragu daga kashi 30 a 1990 zuwa kashi 29 a 2015

Fusata da irin yadda Nigeria ke kamuwa da cututtuka daga grubataccen ruwa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da dokar ta baci akan tsafta da muhallin ruwa (WASH), kamar dai yadda ya bayyana takaicinsa kan yadda kasar ta zamo na 2 a duniya wajen yin kashi a bainar jama'a.

"Kasarmu ce ta biyu a duniya wajen yin kashi a bainar jama'a, kusan kashi 25 na yin ba-haya a bainar jama'a," a cewar shugaban kasar.

A cikin wata sanarwa daga mai bashi shawara na musamman kan kafofin sadarwa da watsa labarai, Mr. Femi Adesina, shugaban kasar ya kaddamar da dokar ta bacin ne a lokacin bukin kaddamar da wani sabon daftari na sake dawowa da shirin tsafta da samar da ruwa na kasa WASH a fadar shugaban kasa, Abuja.

KARANTA WANNAN: Da zafi zafi: Buhari ya kaddamar da dokar ta baci akan tsafta da samar da ruwa a Nigeria

Nigeria ce ta 2 a duniya wajen yin kashi a bainar jama'a - Buhari
Nigeria ce ta 2 a duniya wajen yin kashi a bainar jama'a - Buhari
Asali: Facebook

Buhari ya ce kaddamar da dokar ta bacin ya zama wajibi ne don rage yawaitar cututtukan da ake kamuwa dasu daga ruwa maras tsafta da kuma kazantar muhalli a fadin kasar, a cewar sa, cututtukan da ake samu daga hakan, ya haifar da mutuwar mutane da dama.

"Samuwar bututun raba ruwa ya kai kashi 32 a 1990 amma ya ko,a kashi 7 a 2015; samar da tsaftataccen muhalli ya ragu daga kashi 30 a 1990 zuwa kashi 29 a 2015," a cewar Buhari.

Ya ce: "Hukumar dorewar muradun kargin, na da bukatar cimma (6.1 da 6.2) na shirin WASH, inda a lokacin har ta bukaci tallafi daga WASH don samar da adadin yawan tsaftataccen ruwa a wuraren da ake bukatar hakan cikin farashi mai sauki.

"Ina kira ga dukkanin gwamnatocin jihohi da su yi koyi da wannan mataki da na dauka kamar dai yadda al'adar hakan ta tanadar don bamu damar yin aiki kafada-da-kafada don cimma muradun karni na shirin WASH kafin nan da shekarar 2030," cewar shugaban kasa Buhari.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel