Tirkashi: APC na shirin sauya sunan Ibrahim Shekarau

Tirkashi: APC na shirin sauya sunan Ibrahim Shekarau

Jam’iyyar All Progressives Congress APC shiyar jihar Kano na shirin sauya sunan tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a takarar kujerar Sanatan Kano ya tsakiya,

Jaridar Guardian ce ta rawaito cewa ana son musanya sunan Shekarau da na wani kusa dake tare da Gwamnatin tarayya a kujerar Sanatan Kano ta tsakiya.

Malam Ibrahim Shekarau wanda yayi Gwamnan Kano sau biyu ya sauya Sheka ne daga jam’iyyar PDP zuwa APC tun bayan da tsohon Gwamna kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fita daga APC ya koma PDP.

Tirkashi: APC na shirin sauya sunan Ibrahim Shekarau
Tirkashi: APC na shirin sauya sunan Ibrahim Shekarau
Asali: Facebook

A baya, Mun kawo muku labarincewa Ibrahim Shekarau yayi hira da Jaridar Daily Trust kwanaki inda yayi magana game da yadda zaben badi zai kasance.

Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa an dauki Jam’iyyar PDP an mikawa Rabiu Musa Kwankwaso bayan ya sauya-sheka zuwa PDP. Shekarau yace wannan zalunci yana cikin abin da ya sa ya fice daga Jam’iyyar PDP ya dawo APC.

KU KARANTA: Muna kashe miliyan N3.5m wajen ciyar da Zakzaky kowani wata – Gwamnatin tarayya (Bidiyo)

Tsohon Gwamnan yace ya hakura da takarar kujerar Shugaban kasa a PDP ne har ta kai ya fice daga Jam’iyyar domin ayi sulhu a zauna lafiya a Jihar sa ta Kano. Yanzu dai Malam Shekarau zai nemi kujerar Sanatan Kano a APC.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng