Mutuwa riga: Karanta wata mutuwar ban al’ajabi da wani Fasinja ya yi a filin sauka da tashin jirage

Mutuwa riga: Karanta wata mutuwar ban al’ajabi da wani Fasinja ya yi a filin sauka da tashin jirage

Wani Fasinja dake shirin tafiya a jirgin sama daga filin sauka da tashin jirage na Murtala Muhammed dake jahar Legas ya yanke jiki ya fadi, ya mutu har lahira babu duk babu zagi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito mutumin mai suna Ademola Adelek ya mutu ne jim kadan bayan ya iso filin da misalin karfe 5:30 na safe inda kwatsam ya yanke jiki ya fadi yana ta neman iska, daga nan kuma jama’an dake zagaye da shi suka kai masa dauki.

KU KARANTA: Jama’a da dama sun bata yayin da mayakan Boko Haram sun kai samame cikin dare

Sai dai duk kokarin da jama’an suka yi don ganin sun farfado da Adeleke, hatta a ma’aikatan kiwon lafiya dake filin sun yi iya kokarinsu don ganin sun ceto Adeleke, amma duk da haka bai yi sa’a ba, nan take ya mutu.

Jim kadan bayan faruwan lamarin sai ga motar daukan gawa mallakin hukumar kula da filayen jiragen sama ta daukeshi zuwa asibitin koyarwa ta jami’ar jahar Legas, inda a can ne aka tabbatar da mutuwarsa.

Kaakakin hukumar FAAN, Henrietta Yakubu ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace mamacin ya mutu ne jim kadan bayan isarsa filin sauka da tashin jirage dake jahar Legas. “Daga bisani muka mika shi zuwa Asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarshi.

“Gaskiya bam ji dadi ba, da alama asibiti za shi don duba lafiyarsa a kasar waje, sai ga shi kafin nan ya yanke jiki ya mutu, amma dai bamu da tabbacin wani jirgi zai bi zuwa inda za shi.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel