Yanzu Yanzu: Yan Boko Haram na kaddamar da hari a Yobe

Yanzu Yanzu: Yan Boko Haram na kaddamar da hari a Yobe

A yanzu haka yan ta’addan Boko Haram na kaddamar da hari a garin Katarko, da ke tsawon kilomita 20 zuwa Damaturu, babbar birnin jihar Yobe, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin yankin da ya gudu zuwa wani tudun tsira ya bayyana cewa maharani sun kai mamaya garin a wasu motocin RPG laden Hilux uku da misalin karfe 5:06 na yamma.

“Suna ta hari ba kakkautawa sannan suna cinna wa gidajenmu wuta,” inji shi.

Yanzu Yanzu: Yan Boko Haram na kaddamar da hari a Yobe
Yanzu Yanzu: Yan Boko Haram na kaddamar da hari a Yobe
Asali: Depositphotos

Ya bayyana cewa mazauna yankin da jami’an tsaro sun tsere zuwa wani wajen tsira.

A wani lamari na daban mun ji cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe wani mutum, Alhaji Nasiru Maimasara, a kwatas din Gachi da ke karamar hukumar Kankia a jihar Katsina.

KU KARANTA KUMA: An sallami jami’in dan sandan da ya sha giya ya bugu a cikin wani bidiyo (hoto)

An tattaro cewa ‘yan bindiga sun sace ‘yar mutumin a yayin da ta ke yunkurin guduwa daga inda lamarin ya afku.

Rahoton ya nuna cewa abun ya faru ne da misalin karfe 2:00 na daren ranar Talata, 6 ga watan Nuwamba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel