Abu kamar almara: Yarinya mai shekaru 10 ta kashe jariri ta hanyar tattaka kansa

Abu kamar almara: Yarinya mai shekaru 10 ta kashe jariri ta hanyar tattaka kansa

Rahotanni da muke samu daga kamfanin jaridar Metro Uk na kasar Burtaniya, na nuni da cewa, wata yarinya mai shekaru 10 da haihuwa, ta gurfana gaban kotu, bisa zarginta da aikata laifin kisan wani jariri mai watanni 6 da haihuwa, a wata cibiyar raino da ke kasar Amurka.

Yarinyar, wacce ake tuhuma da aikata kisan mummuke da gangan, an yi zargin ta yi tsalle tare da dira akan kan yaron. Kamar dai yadda rundunar yan sanda ta bayyana cewa sun samu kiran waya daga masu kula da cibiyar akan yadda jini ke bulbulowa daga kan yaron.

Jim kadan bayan da aka garzaya da yaron asibitin St Paul Minnesota, yaron ya amsa kiran mahalicci.

KARANTA WANNAN: 2019: Har yanzu al'ummar Igbo ba su cimma matsaya tsakanin Buhari da Atiku ba - Isiguzo

Abu kamar almara: Yarinya mai shekaru 10 ta kashe jariri ta hanyar tattaka kansa
Abu kamar almara: Yarinya mai shekaru 10 ta kashe jariri ta hanyar tattaka kansa
Asali: Getty Images

Rundunar yan sanda ta ce an tambayi wasu kananan yara 4 da kuma wani babba daya, akan yadda lamarin ya kasance, wadanda suka nuna yarinyar a matsayin wacce ta aikata laifin, hakan ya sa aka cafke ta, inda ta amince da aikata laifin taka kan nasa.

Jami'in rundunar yan sandan na shiyyar Chippewa, Jim Kowalczyk, ya ce yaron ya gwara kansa ne da wani abun tsayar da yara, wanda ya sa shi soma kuka, kukan ne kuma ya baiwa yarinyar haushi, har ta tattaka kan nasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel