Sojojin Najeriya zabi ne, a munada makamai, ba zasu iya fuskantarmu ba – Kungiyar Shi’a

Sojojin Najeriya zabi ne, a munada makamai, ba zasu iya fuskantarmu ba – Kungiyar Shi’a

Mambobin Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da akafi sani da akidar sun bayyana cewa jami’an sojoju ba zasu uya fuskantarsu ba da suna da makamai.

Kungiyar ta bada wannan jawabi ne a ranan Litinin a wani hira da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Abdullahi Zango, wanda shine shugaban kungiyar ya ce jawabin da hukumar soja da yansanda suka saki kan kisan gillan da akayi musu karerayin banza ne domin kare kansu.

KU KARANTA: Wasu ja’irai za su yi wa INEC kutse a lokacin zaben 2019 inji wasu Kunguyoyi

Zango yace: “Sun kasance suna cewa muna rike da makamai, wannan babban karya ne. da muna da makami, hukumar soji ba zasu iya fuskantarmu ba.”

“Da munada makamai, sojoji sun yi mana kadan. A yanzu ma da irin karfin halin da muke da shi, babu makamai amma suna guduwa, balle ace munada makamai.”

Sun san bamu da makamai saboda matsoratan banza ne.”

Sojojin Najeriya zabi ne, a munada makamai, ba zasu iya fuskantarmu ba – Kungiyar Shi’a
Sojojin Najeriya zabi ne, a munada makamai, ba zasu iya fuskantarmu ba – Kungiyar Shi’a
Asali: Facebook

Zango ya tuhumci hukumar yan sanda da amfani da wasu mutane masu makamai a cikin kungiyarsu domin bata musu suna.

Kawo zuwa yanzu, ya yi ikirarin cewa sun biya N8million kudin jinyan yna shi’a 106 a asibitoci daban-daban a birnin tarayy Abuja. Baya ga haka, ana bukatar Karin N25 million domin kula da wasu wadanda suka jikkata.

Ya karashe da cewa zuwa yanzu, mambobin kungiyar 47 ne suka rasa rayukansu sakamakon arangam da jami’an tsaro.

anarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng