Karin albashi: Dalilin da ya sa ba za mu iya biya wa ma’aikata bukatun su ba - Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta bayyana abin da ya sa ba za ta iya biya wa ma’aikata bukatun su na kara albashi mafi aranci zuwa naira 30,000 ba.
Kungiyoyin kwadago dai sun sha alwashin shiga yajin aiki na kasa baki daya a gobe Talala, 6 ga watan Otoba muddin gwamnatin tarayya ta ki biya musu bukatun su.
Babban sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce damuwar gwamnatin tarayya ba wai jin dadin ma’aikatan kasar nan ne abubuwan da ke kan ta ba kadai ba, akwai sauran abubuwan da za a yi la’akari da su domin za su shafi tattalin arzikin kasa.

Asali: Facebook
Sannan kuma cewa akwai batun yadda ko da an yi karin albashin, to darewar biyan ma abin dubawa ne, domin akwai jihohi da dama wadanda su naira 18,000 da ake biya a yanzu ma sai an kai ruwa rana suke iya biya, wasu kuma ba su ma iya biyan hakan.
KU KARANTA KUMA: Atiku zai je kasar Amurka a karshen Nuwamba - Okupe
Ya yi nuni da cewa jihohi 27 a halin yanzu su na shan wahala wajen biyan naira 18,000 da ake biya a halin yanzu, wadda kungiyar kwadago ta raina, ta ke neman kari.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng