Alkawaran Gwamnatin Tarayya duk kanzon kurege ne - ASUU
- ASUU sun bayyana alkawaran Gwamnatin Tarayya a matsayin kanzon kurege, cewa mambobinta ba za su bi ta kansu ba
- Kungiyar ta ce hukuncinta na umurtan mambobinta a fadin kasar na su ajiye kayan aiki a ranar Lahadi ya kasance saboda rashin kula da daukar nauyin makarantun jami’ar kasar
- Shugaban kungiyar ya kuma koka akan rage kasafin hukumar ilimi da aka yi a yan shekarun nan, inda yace hukumar ilimi na kowacce kasa ta aka fi ba muhimmanci
Kungiyar malaman jami’a (ASUU) sun bayyana alkawaran Gwamnatin Tarayya a matsayin kanzon kurege, cewa mambobinta ba za su bi ta kansu ba.
Shugaban ASUU, Farfesa Abiodun Ogunyemi, ya fadi hakan a ranar Litinin, 5 ga watan Nuwamba a lokacin wani hira da Channels Television’s a shirin Sunrise Daily.
“Mun yanke shawarar cewa alkawaran gwamnati kanzon kurege ne. Bamu damu da kowani alkawari gwamnati za ta yi ba a yanzu,” inji shi.

Asali: Twitter
Furucin Ogunyemi na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan kungiyar ta dauki hukunci sakamakon hanzukansu da Gwamnatin Tarayya.
KU KARANTA KUMA: APC ta yi kira ga a binciki ziyarar da Atiku ya kai Dubai
A cewar ASUU, hukuncinta na umurtan mambobinta a fadin kasar na su ajiye kayan aiki a ranar Lahadi ya kasance saboda rashin kula da daukar nauyin makarantun jami’ar kasar.
Ya kuma koka akan rage kasafin hukumar ilimi da aka yi a yan shekarun nan, inda yace hukumar ilimi na kowacce kasa ta aka fi ba muhimmanci.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng