Dandalin Kannywood: Wata fitacciyar jarumar fina-finan Hausa na kwance a asibiti ba lafiya

Dandalin Kannywood: Wata fitacciyar jarumar fina-finan Hausa na kwance a asibiti ba lafiya

- Wata fitacciyar jarumar fina-finan Hausa na kwance a asibiti

- Fitacciyar jarumar bata lafiya

- Sunan jarumar Maryam Gidado

Shahararriyar jarumar nan da tauraronta ke hasanakawa a masana’antar Kannywood, Maryam Gidado wacce akafi sani da Maryam Babban Yaro yanzu haka tana kwance a asibiti tana karbar kulawar likita sakamakon rashin lafiyar da take fama da ita.

Dandalin Kannywood: Wata fitacciyar jarumar fina-finan Hausa na kwance a asibiti ba lafiya
Dandalin Kannywood: Wata fitacciyar jarumar fina-finan Hausa na kwance a asibiti ba lafiya
Asali: Facebook

KU KARANTA: Wata budurwa ta bada labarin yadda ta kubuta daga hannun matsafa a Najeriya

Duk da dai har yanzu ba'a san takamaiman abun da ke damun ta ba, amma dai tana cikin wani mawuyacin halin da take bukatar addu'a daga dukkan al'umma maza da mata masoyan ta.

Legit.ng Hausa ta tuna cewa a baya jarumar ta yi tsokaci akan wani babi day a shafi rayuwarta inda ta bayyana cewa ita bazawara ce domin ta taba yin aure har sau biyu.

Jarumar ta bayyana cewa anyi mata auren fari tana da shekaru 13 a duniya kasancewarta Bafulatanar asali.

Ta kuma haifi ‘Yarta ta farko tana da shekaru 14 bayan shekara daya da aurar da ita ga mijin nata na fari.

Ta kuma kara yin aure inda anan ne ta haifi ‘Danta na biyu,sannan kuma ta bayyana cewa alokacin da take da cikin ‘Dan nata na biyu ne sai mijin ya gudu ya bar ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel