Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa Sarkin Awe, Abubakar Umar II rasuwa
Allah ya yiwa Alhaji Abubakar Umar II, Sarkin Awe da ke Jihar Nasarawa rasuwa.
Hadimin gwamnan Umaru Al-Makura kan yada labarai, Mr Yakubu Lamai ne ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai (NAN) rasuwar a birnin Lafia.
Ya ce basaraken mai daraja ta daya ya rasu ne a safiyar yau Asabar a wani asibiti da ke Abuja.
Ya ce basaraken ya rasu bayan ya yi fama da 'yar gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 69 a duniya bayan ya kwashe shekaru 33 a kan kujerar sarautar Awe.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Hotunan jana'izar Janar Idris Alkali da aka gudanar a Abuja
A sakon ta'aziyarsa, gwamna Al-Makura ya bayyana cewar ya girgiza da jin labarain rasuwar sarkin wanda ya kasance mutum ne mai kaunar zaman lafiya da hada kan al'umma.
Ya yi kira da al'ummar jihar suyi amfani da rasuwar sarkin a matsayin dama da za su yiwa junansu afuwa kana su kara tabbatar da zaman lafiya a jihar.
NAN ta ruwaito cewar an yi jana'izar sarkin kamar yadda koyarwar addinin islama ta tanada.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng