Ba mu zalunci 'yan Shi'a ba, rahoton Amnesty karya ne - Rundunar 'Yan Sanda

Ba mu zalunci 'yan Shi'a ba, rahoton Amnesty karya ne - Rundunar 'Yan Sanda

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi watsi da zargin da kungiyar Amnesty International ta yi na cewa jami’anta sun harbe da raunata mabiya Shi’a a yayin da suke tattaki a Abuja.

Rundunar ‘yan sandan ta ce babu gaskiya a bayanan da ke kunshe a cikin rahoton da Amnesty ta fitar, Illa wani yunkuri na karkatar da hankali kan ta’asar da mabiya El Zakzaky suka yi wanda ya hada da kai wa jami’an tsaro hari.

A ranar Laraba, 31 ga watan Oktoba ne Amnesty ta fitar da rahoto kan artabun da aka yi tsakanin ‘yan shi’a da jami’an tsaro inda a ciki ta ce bincikenta ya nuna cewa amfani da karfin da ya wuce kima da sojoji da ‘yan sandan Najeriya suka yi ne ya kai ga rasa rayuka da dama.

Ba mu zalunci 'yan Shi'a ba, rahoton Amnesty karya ne - Rundunar 'Yan Sanda
Ba mu zalunci 'yan Shi'a ba, rahoton Amnesty karya ne - Rundunar 'Yan Sanda
Asali: Twitter

Rundunar ‘yan sandan tace rahoton na Amnesty wani yunkuri ne na karkatar da hankali ga saba doka da munanan laifukan da mabiya Ibrahim El Zakzaky suka aikata wadanda ta ce sun kunshi kai wa jami’anta hari da kona motar ‘yan sanda a Abuja a ranar 30 ga wata tare da haifar da tashin hankali a sassan birnin.

KU KARANTA KUMA: Amurka ta yi martani kan rikicin sojoji da ’yan Shi’a

Ta ce duk da abun da yan shi'an suka yi, amma hakan bai sa ta yi amfani da karfi ba kan ‘yan shi’ar amma ta yi kokarin cafke mambobin kungiyar 400 da ta kama dauke da makamai da suka hada da bom da miyagun kwayoyi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng