Atiku Abubakar yayiwa Shugaba Buhari wankin babban bargo
Dan takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2019 mai zuwa karkashin tukar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayiwa Shugaba Buhari kaca-kaca game da kudurin gwamnatin sa na sayar da kadarorin kasa da nufin gudanar da kasafin kudin shekarar 2019.
Atiku Abubakar din dai yayi wannan kalaman ne a cikin wata sanarwa da ofishin yakin neman zaben sa ya fitar a Abuja inda suka ce sayar da kadarorin na gwamnatin tamkar kaiwa kololuwa ne a rashin sanin yakamata ta gwamnatin Shugaba Buhari.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Da wuya Buhari ya iya kada Atiku a 2019 - Wani dan APC
Legit.ng Hausa ta kuma samu cewa sanarwar har ila yau ta kuma ce kudurin gwamnatin ta Buhari na sayar da kadarorin ya kuma kara fito da rashin gaskiyar ta ne karara domin kuwa kusan duka kadarorin da suke cewa za su sayar gwamnatin PDP ce ta assasa su.
Wannan a cewar sanarwar tamkar tufka da warwara ne musamman ma ganin yadda jam'iyyar su ta APC ke cewa gwamnatin ta PDP bata yiwa kasa komai ba a cikin shekaru 16 da tayi tana mulki a Najeriya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng