Najeriya da kasashe 69 za su halarci taron Ilimi a Kasar India
Kimanin wakilai 200 daga kasashe 70 na nahiyyar Afirka, Asia da kuma daular Larabawa ta Tsakiya, za su hallara a birnin New Delhi domin halartar taron inganta harkokin ilimi na jami'o'i karo na 14 da za a gudanar a kasar India.
Dakta Saravana Kumar, babbar sakatariyar cibiyar ilimi ta kasar India, ita ta bayyana hakan a ranar Talatar da ta gabata kamar yadda shafin jaridar Vanguard ta ruwaito.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, za a gudanar da wannan gagarumin taro domin karfafa gwiwar gwamnatocin kasashen wajen bunkasa inganci na harkokin ilimi musamman na jami'o'i.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, cibiyar kasuwanci da masana'antu tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar India, suke da alhakin daukar nauyin wannan babban taro domin inganta tsare-tsare da dangartakar ilimi dake tsakanin kasashen na duniya.

Asali: Depositphotos
Dakta Kumar ta bayyana cewa, adadin wakilan kasashen da za su halarci wannan taro zai bayar da kofa bude ga dukkanin masu ruwa da tsaki wajen inganta dangartarka da ingancin ilimi a tsakanin kasashen duniya baki daya.
KARANTA KUMA: Farashin Man Fetur yana nan a N145 - NNPC
Kazalika shugaban jami'ar Katsina ta Umaru Musa Yar'Adua University, Farfesa Idris Funtua, ya yi kira kan tashi tsaye wajen fuskantar barazana da ta yi katutu a fannin ilimi na kasar nan.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammad Buhari bayan da dawowarsa aga jihar Kaduna ya kuma shiga bayan Labule da wasu gwamnoni hudu na jam'iyyar PDP reshen Kudu maso Kudancin kasar a fadarsa ta Villa dake babban birnin tarayya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng