Ya zama dole gwamnati ta rungumi tsarin kayyade haihuwa sannan ta hana almajiranci - Sarki Sanusi

Ya zama dole gwamnati ta rungumi tsarin kayyade haihuwa sannan ta hana almajiranci - Sarki Sanusi

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi, ya yi kira ga gwamnati a dukkan mataki da ta kayyade yawan haihuwa a kasar.

Ya bayyana cewa hakan na da matukar muhimmanci musamman a yankin arewacin kasar inda yawan daliban da basa zuwa makaranta ya munana.

Sanusi ya kuma bayyana cewa akwai bukatar yan arewa su mayar da wasu daga cikin masallatai a wasu yankunan wuraren koyon karatu.

Ya zama dole gwamnati ta rungumi tsarin kayyade haihuwa sannan ta hana almajiranci - Sarki Sanusi
Ya zama dole gwamnati ta rungumi tsarin kayyade haihuwa sannan ta hana almajiranci - Sarki Sanusi
Asali: Depositphotos

Sarkin ya bayyana hakan ne a taron yaye dalibai na jami’ar Nile da ke Najeriya, Abuja, inda dalibai 21 suka kammala da digiri mafi girma cikin dalibai 365 da suka kammala karatu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dan majalisar dokokin jihar Ekiti da yan bindiga suka harba ya mutu

Tsohon gwwamnan babban bankin na Najeriya (CBN) wanda ya ga laifin iyaye kan haifar yara da yawa wanda ba za su iya daukar nauyinsu ba kuma caccaki gwamnati kan gazawarta wajen magance matsalar hukumar ilimi da kuma neman mafita mai dorewa akan matsalar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta karyata rahotannin da ke yawo na cewar gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari, zata kakaba tsarin kayyade adadin 'yayan da maya zasu haifa a kasar.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter, @ZShamsuna, Ahmed ta ce, gwamnati na kokarin karfafa guiwar shuwagabannin addinai dana gargajiya don fadakar da jama'arsu dangane da muhimmancin bada tazarar haihuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng