Da dumin sa: Aikin jigilar matafiya na jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya tsaya

Da dumin sa: Aikin jigilar matafiya na jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya tsaya

Shugaban hukumar gwamnatin tarayya dake kula da harkokin jigilar matafi na jirgin kasa watau Nigeria Railway Corporation, NRC, mai suna Fidet Okhiria, ya sanar da tsayar da ayyukan jigilar matafiyan daga garin Kaduna zuwa Abuja har illa-ma-sha'Allahu.

Mista Fidet Okhiria ya bayyana cewa wannan matakin da hukumar ta dauka ta dauke shi ne duba da halin rashin tsaron da jihar ke fama da shi a halin yanzu kuma za su cigaba da zaran komai ya daidaita.

Da dumin sa: Aikin jigilar matafiya na jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya tsaya
Da dumin sa: Aikin jigilar matafiya na jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya tsaya
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta samu cewa sakamakon rikicin da ake yi a jihar ta Kaduna, gwamnatin jihar a kwanan baya ta saka dokar ta baci a jihar na tsawon kwanaki kafin ta dan sassauta ta bayan samun zaman lafiya a wasu sassan jihar.

A wani labarin kuma, Da alamu dai rikicin cikin jam'iyyar dake mulki a Najeriya, ta All Progressives Congress (APC) zai dauki wani sabon salo biyo bayan labaran da muke samu na kammala shirye-shiren ficewa daga jam'iyyar da gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun yayi.

Binciken da majiyar mu ta jaridar Punch tayi dai ya bayyana cewa gwamnan yana sunsunar jam'iyyar adawa ta Democratic Peoples Party (DPP) ne kuma tuni har ma wasu makusantan sa da abokan siyasar sa sun soma shiga jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng