Zigidir suka yi mata kan tana takara a PDP a jiharta ta Binuwai
- Wata mata ta bayyana yanda akayi mata zundur a filin zabe
- Anyi amfani da yan daba don tada hargitsi a wajen
- Sannan an canja jerin abubuwan da aka bamu

Asali: Twitter
Wata mata wadda ta tsaya neman takarar majilisar jaha ta bayyana yanda akayi mata zundur a cikin jama'a a lokacin da ake gudanar da karamin zaben a jahar Benue.
"Nazo na tarar da taron mutane sun zagaye wakili na suna ta dukansa ,kafin na farga sun rufeni da duka suka yayyaga kayana sukamin zundur a cikin mutane".
Tace tana zargin abokin karawarta da yin amfani da yan daba don tada hargitsi a wajen zaben .
Wasu daga cikin yan daban sun tafi suna neman wakili na yayin da wasu suka nufi wajen women leader da vice chairman na yankin suka ce matukar suka zabe ni tofa zasu yanke musu 'yan yatsu.
Sunje wajen maiyi mini kamfe sukaja masa kunne a yayinda nake tsaye a wajen basusan cewa nice ba,sannan suka ambaci sunan jagoran nasu sukace shine ya aiko su.
DUBA WANNAN: Sau 600 aka fasa bututun mai a kudu a bana - NNPC
Sannan da muka shiga ciki sai muka tarar an canja sunayen wadanda aka bawa shugabancin wajen.
Wannan shine abinda na fuskanta na nuna kaskanci da tozartawa,saboda wasu mutanen suna ganin sune yafi dacewa dasu hau wannan matsayi bani Ba.
Ina kira ga duk wata kungiya da kuma yan Nageriya da suyi duba akan wannan lamari,bazamu bari hakan taci gaba da faruwa ba akan mata.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng