Hukumar Sojin Kasa za ta fara kera Motocin Yaki a 2025 - Buratai

Hukumar Sojin Kasa za ta fara kera Motocin Yaki a 2025 - Buratai

Za ku ji cewa a yau Asabar shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa a shekarar 2025 mai gabatowa hukumar sojin za ta fara kera-keren Motocin yaki a kasar nan ta Najeriya.

Buratai ya bayyana hakan ne yayin yaye sabbin kananan dakarun sojin kasa a cibiyar makarantas horas da dakarun soji ta Nigerian Army Depot dake garin Zaria na jihar Kaduna.

Shugaban hafsin sojin ya bayyana cewa, a halin yanzu cibiyar dakarun dake garin Zaria cikin kwazonta na binciken kimiyya da fasaha ta kera wasu Motoci biyar na sintiri da ta cancanci yabo dangane da wannan hobbosa na ci gaba da ta aiwatar.

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ta ruwaito, wannan kwazo na cibiyar zai tallafawa hukumar dakarun sojin kasa ta Najeriya wajen cin gashin kanta inda a shekarar 2025 za ta fara kera wasu nau'ika na motocin yaki.

Hukumar Sojin Kasa za ta fara kera Motocin Yaki a 2025 - Buratai
Hukumar Sojin Kasa za ta fara kera Motocin Yaki a 2025 - Buratai
Asali: Depositphotos

Kazalika shugaban hafsin sojin kasan ya taya murna ga sabbin dakarun sojin da a cewar sa bikin yayewarsu ya yi daidai da lokacin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar barazana da kalubalai na tsaro.

KARANTA KUMA: Wani Wanzami ya murkushe Budurwa 'Yar 14 a jihar Legas

Janar Buratai ya nemi dakarun akan jajircewa da nuna kwarewa bisa aiki tare da yiwa kundin tsarin mulkin kasar da'a ta koluluwa a duk inda suka tsinci kawunan su.

Ya kuma yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da goyon bayansa ga hukumar da taka rawar gani bisa ga nasarorin da hukumar ta samu wajen yakar ta'addanci a fadin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng