Ka tsaya matsayinka kada zancen duniya ya rude ka - Shehu Sani ya gargadi Ekweremadu

Ka tsaya matsayinka kada zancen duniya ya rude ka - Shehu Sani ya gargadi Ekweremadu

- Kwamred Shehu Sani, ya gargadi Ike Ekweremadu, akan kada ya kuskura ya fita daga jam'iyyar hamayya ta PDP zuwa wata jam'iyya ta daban

- Sanatan, wanda ya yi murabus daga jam'iyyar APC, ya bayyana wannan gargadi nasa bayan jin wata jita-jita da ke cewa Mr. Ekweremadu na shirin barin PDP zuwa APC

- A hannu daya kuwa, Mr Ekweremadu ya karyata rahotannin da ke yawo na cewar yana shirin fiewa daga PDP zuwa jam'iyyar APC

Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya gargadi mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ike Ekweremadu, akan kada ya kuskura ya fita daga jam'iyyar hamayya ta PDP zuwa wata jam'iyya ta daban.

Sanatan, wanda ya yi murabus daga jam'iyyar APC, ya bayyana wannan gargadi nasa a cikin wata sanarwa, bayan jin wata jita-jita da ke cewa Mr. Ekweremadu na shirin ficewa daga PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

Kamar yadda Kwamred Shehu sani ya wallafa a shafinsa na Twitter, yana mai cewa: ''Abokina Ike, ka tsaya matsayinka kada zancen 'yan duniya ya rude ka, nima dai kaga na ficewa, idan kuma kaki ji, to ba ka ki gani ba."

KARANTA WANNAN: Ganduje ya gayyacin limaman jihar Kano kan bidiyon da ke nuna shi yana karbar cin hanci

Ka tsaya matsayinka kada zancen duniya ya rude ka - Shehu Sani ya gargadi Ekweremadu
Ka tsaya matsayinka kada zancen duniya ya rude ka - Shehu Sani ya gargadi Ekweremadu
Asali: Twitter

A ranar 20 ga watan Oktoba, Mr Sani ya bada sanarwar ficewarsa da jam'iyyar APC. Wannan mataki nasa ya biyo bayan kwanaki kadan da uwar jam'iyyar APC ta kasa ta bayar da sunan hadimin Gwamna Nasri El-Rufai, Uba Sani, a matsayin dan takarar ta na sanatan Kaduna ta tsakiya a zaben 2019.

Shehu Sani ya koma jam'iyyar People’s Redemption Party (PRP), kwanaki uku da ficewarsa daga APC

KARANTA WANNAN: Nazari kan jihohin da jam'iyyar APC za ta iya rasawa a zaben 2019

A hannu daya kuwa, Mr Ekweremadu ya karyata rahotannin da ke yawo na cewar yana shirin fiewa daga PDP zuwa jam'iyyar APC. Ya karyata rahoton hakan ne a shafinsa na Facebook, a safiyar ranar Laraba 24 ga watan Oktoba, 2018.

"Ina so kowa ya san alkiblar siyasata, tana hannun Ubangiji mai kowa mai komai, wanda ya dade yana saukarmin da alkairan sa. Ina godiya ga Allah matuka akan ni'imomin da ya ke saukar min," kamar yadda Ekweremadu ya wallafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng