Faransa za ta fara koyar da darasin 'Larabci' a makarantun gwamnatin kasar
- Gwamnatin shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, na kokari don karfafa guiwar makarantu na koyar da darasin 'Arabi' ga dalibai tun daga shekaru 6
- Gwamnatin kasar Faransa ta ce dubunnan yara na zuwa makaranta ne karkashin daukar nauyin kasashen da ke magana da yaren Larabci, a cewar jaridar WSJ
- Wasu daga cikin makarantu masu zaman kansu sun samar da masallatai don baiwa dalibai Musulmai damar koyon yaren Larabci da kuma haddace Al-Qur'ani mai girma
Kasar Faransa za ta fara koyar da darasin 'Arabi' a makarantun gwamnati na kasar don horas da dalibai dangane da harkokin addini, wanda shine hanya mafita ga makarantun da ke dauke da Musulmai a cikin kasar.
Gwamnatin shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, na kokari don karfafa guiwar makarantu na koyar da darasin 'Arabi' ga dalibai tun daga shekaru 6, kamar dai yadda jaridar The Wall Street Journal ta kasar ta wallafa rahoton hakan a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN: NDLEA: Kafin haramta 'Codeine', Kano, Jigawa sun sha kwalba Miliyan 3
Wannan shawarar ta zo ne sakamakon yadda wasu jami'an gwamnatin Faransa suka gano cewa akwai karancin koyar da darasin a makarantun gwamnatin kasar wanda kuma hakan ya haifar sabani tsakanin Kirista da Musulmai wadanda sune masu karancin yawa a kasar.

Asali: UGC
Gwamnatin kasar Faransa ta ce dubunnan yara na zuwa makaranta ne karkashin daukar nauyin kasashen da ke magana da yaren Larabci, a cewar jaridar WSJ.
Wasu daga cikin makarantu masu zaman kansu sun samar da masallatai don baiwa dalibai Musulmai damar koyon yaren Larabci idan har malamin nada cikakken sani akan yaren yayin da kuma ake horas da wasu yadda zasu haddace Al-Qur'ani mai girma.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng