Femi Adesina: Maganar karin albashi mafi karanci zuwa N30,000 ba mai yiyuwa bane
- Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce maganar karin mafi karancin albashi ga ma'aikata har zuwa N30,000 ba abu ne mai sabuwa ba
- Kungiyar kwadago dai ta yi watsi da kudirin gwamnatin tarayyarna karin albashi mafi karanci zuwa N24,000 daga N18,000
- Ya ce a halin da ake ciki yanzu, wasu gwamnonin ba sa iya biyan N18,000, to ballantana ace an maida shi N30,000
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce maganar karin mafi karancin albashi ga ma'aikata har zuwa N30,000 ba abu ne mai sabuwa ba. Wannan kuwa ya biyo bayan matsin lambar da gwamnatin tarayya ke samu daga kungiyoyin kwadago na karin albashin.
Kungiyar kwadago dai ta yi watsi da kudirin gwamnatin tarayyarna karin albashi mafi karanci zuwa N24,000 daga N18,000.
Da ya ke jawabi a wani shiri na musamman da gidan talabijin na Channels TV ya gudanar, Adesina ya ce koda ace ma'aikata za su sadaukar da gaba daya albashinsu, hakan ba zai samar da makudan kudaden karin albashin da ake muradi ba.
KARANTA WANNAN: Tozarci ne karara kalaman Buhari na 'Yan Nigeria masu wata to su koma can' - PDP

Asali: UGC
Ya ce a halin da ake ciki yanzu, wasu gwamnonin ba sa iya biyan N18,000, to ballantana ace an maida shi N30,000.
"Don jaka idan har ba zasu iya biyan N18,000 ba, kuma Kungiyar kwadago ta ci gaba da bukatar karin albashi mafi karanci zuwa N30,000 kuma suka ki yarda su sauko da farashin, to kuwa za a samu babban tsaiko, wanda ba zai yiwa kowa a kasar dadi ba," a cewar sa.
"Ina tunanin, akwai makoma mai kyau idan aka zauna akan teburin sasanci, ba wai kungiyar kwadago ta dage lallai sai N30,000 ba."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng