Oshiomhole dan jagaliya ne, bai cancanci shugabancin APC ba – Gwamna Akeredolu
Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya fayyace gaskiya akan zarginsa da aka yi na cewa shi da wasu gwamnoni na kulla munakisa don tsige Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole.
Duk da cewa ya karyata zargin da ake yi masa, sai dai ya jadadda cewa Oshiomhole dan jagaliya ne, wanda ya haritsa jam’iyyar APC a cikin lokaci kankani a yayin zabukan fidda-gwani na jam’iyyar da aka gudanar farkon watan Oktoba.
A cikin wata takardar da hadiminsa kan Ayyuka na Musamman, Doyin Odebowale ya fitar ga manema labarai, Akeredolu ya bayyana cewa Oshiomhole dan tayar da zaune tsaye ne, wanda ya haritsa jam’iyyar APC.
Ya zargi Oshiomhole da kawo rudani a zaben fidda yan takara da jam'iyyar ta gudanar a fadin kasar, wanda a sanadiyar hakan rikici ya ki ci yaki cinyewa a cikinta.

Source: Facebook
Gwamnoni da dama sun yi korafi akan yadda Kwamitin Gudanarwa na Kasa na APC ya baddala sunayen ‘yan takara da yawa wadanda ya mika wa hukumar zabe.
KU KARANTA KUMA: Rikicin Kaduna: El-Rufai ya yi barazanar daukar mataki a kan sarakunan gargajiya
Gwamnan ya ce bai taba shirya wani zama na neman a tsige Oshiomhole daga shugabancin jam’iyya ba.
Amma hakan ba zai hana ya nemi a tsige shi din ba, domin bai iya shugabanci ba, bai kuma cancanta ya zama shugaban jam’iyya ba.
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Lagit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng