Keyamo ya ce lallai Atiku mutun ne mai rashawa a gaban kwamitin majalisar dattawa

Keyamo ya ce lallai Atiku mutun ne mai rashawa a gaban kwamitin majalisar dattawa

Kakakin kungiyar kamfen din Shugaan Kasa Muhammadu Buhari, Festus Keyamo a jiya Laraa, 24 ga watan Oktoba ya ce lallai dan takarar jam’iyyar Adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar mutun ne mai cin hanci da rashawa.

Keyamo wanda ya kasance daya daga cikin wadanda za’a tantance a hukumar Nigerian Deposit Insurance Corporation (NDIC), ya yi maganan ne a lokacin da ya gurfana a gaban kwamitin ankuna, da sauran hukumomin kudi na majalisar dattawa.

Shirin ya so zama siyasa lokacin da shugaban kwamitin, Rafiu Ibrahim ya bukaci Keyamo da ya yi bayani idan zai iya ajiye son rai idan aka tabbatar da shi a matsayin mama na hukumar NDIC, kasancewarsa kakakin kungiyar kamfen na APC kuma lauyan EFCC.

Keyamo ya ce lallai Atiku mutun ne mai rashawa a gaban kwamitin majalisar dattawa
Keyamo ya ce lallai Atiku mutun ne mai rashawa a gaban kwamitin majalisar dattawa
Asali: Depositphotos

Ya ce Keyamo ya kira Atiku da mai cin hanci da rashawa sannan cewa yana kokwanto idan zai iya isar da aikinsa yadda ya kamata idan aka tabbatar da shi.

KU KARANTA KUMA: INEC za ta sanar da yan takarar shugaban kasa da na majalisar dokoki a yau

Sai dai Keyamo wanda ya kasance babban lauya yace a zai yi son ransa ba idan har aka tabatar da shi.

Lokacin da Keyamo yayi kokarin yin ayani akan dalilin da ya say a kira Atiku da mai rashawa, Ibrahim ya taka masa birki cewa kada ya je nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Lagit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng