Gwamnatin Buhari za ta kayyade adadin 'yayan da kowacce uwa zata haifa
- Gwamnatin tarayya ta ce tana aiki tukuru don bullo da wani sabon tsari da zai kayyade yawan adadin 'yayan da kowacce uwa zata haifa a Nigeria
- Ta bayyana cewa an sanya shuwagabannin addinai dana gargajiya dake a fadin kasar a cikin shirye shiryen bullo da tsarin
- Sabon tsarin zai taimaka ainun wajen dorewar tattalin kasancewar tsarin zai samar da tattalin arziki kwatankwacin yawan 'yan kasar da kuma sama da shi
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tabbatar da cewa tana aiki tukuru don bullo da wani sabon tsari da zai kayyade yawan adadin 'yayan da kowacce uwa zata haifa a Nigeria.
Ta bayyana cewa an sanya shuwagabannin addinai dana gargajiya dake a fadin kasar a cikin shirye shiryen bullo da tsarin, tana mai cewa yunkurin hakan zai taimaka wajen kawo karshen barazanar da kasar ke fuskanta ta fannin tattalin arzikin kasa da sakamakon yawan 'yan jama'ar kasar.
Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan a lokacin da take amsa tambayoyi a wani taro na tattalin arzikin Nigeria karo na 24 a Abuja, tana mai nuni da cewa yawan 'yan Nigeria na daga cikin manyan dalilan da ya sa har zuwa yanzu kasar bata samu damar farfadowa daga durkushewar tattalin arziki ba.
KARANTA WANNAN: Sabon rahoto: Dan sanda ya kashe diyar tsohon minista saboda taki bude masa kofar motarta

Asali: UGC
Ahmed ta ce, "Mun dau tsawon lokaci muna tuntubar shuwagabannin gargajiya dana addinai. Musamman, mun gano cewa babbar barazanar da ci gaban tattalin arzikin kasar ERGP ke fuskanta, bai wuce yawan jama'ar kasar ba, dole mu saka masarautun gargajiya a cikin sabon tsarin.
"Kuma muna fatan zasu bamu gagarumar gudunmowa da goyon bayansu, zamu yi kokari muga cewa mun bullo da sabon tsari na kayyade adadin yawan 'yayan da kowacce uwa zata haifa saboda muhimmanci dorewar tattalin arzikin kasar."
Ko da aka tambayeta dangane da dorewar tattalin arzikin kasae ERGP da gwamnatin Buhari ke kokarin tabbatarwa, Ahmed ta tabbatar da cewa wannan sabon tsarin zai taimaka ainun wajen dorewar tattalin kasancewar tsarin zai samar da tattalin arziki kwatankwacin yawan 'yan kasar da kuma sama da shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng