Rikicin makiyaya da manoma: Mutane 6 sun samu rauni a garin Adamawa

Rikicin makiyaya da manoma: Mutane 6 sun samu rauni a garin Adamawa

- Hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Adamawa ta tabbatar da cewar an raunata mutane shida a kauyen Chambaji

- Hakan ya biyo bayan rikici da ya kaure tsakanin manoma da makiyaya

- A yanzu an ce zaman lafiya ya dawo yankin yayinda yan sanda ke bincike akan lamarin

Hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Adamawa (ADSEMA) ta tabbatar da raunata mutane shida da aka yi a rikicin makiyaya da manoma a kauyen Chambaji, Yolde-Pate dake karamar hukumar Yola ta kudu.

Muhammad Sulaiman, babban sakataren hukumar, ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Talata, 23 ga watan Oktoba a Yola.

Rikicin makiyaya da manoma: Mutane 6 sun samu rauni a garin Adamawa
Rikicin makiyaya da manoma: Mutane 6 sun samu rauni a garin Adamawa
Asali: Depositphotos

Sulaiman ya bayyana cewa anyi nasarar daidaita lamarin sannan an kwashi wadanda abun ya shafa zuwa asibitin Yolde-Pate domin samun kulawar likita.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Cikin sauki za mu lallasa APC – PDP

Hakazalika lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar yan sandan jihar Adamawa, Othman Abubakar ya tabbatar da lamarin cewa zaman lafiya ya dawo a yankin.

Abubakar ya kuma shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa yan sanda na bincikar lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng