Sheikh Isa Ali Pantami yayi magana game da rikicin garin Kaduna

Sheikh Isa Ali Pantami yayi magana game da rikicin garin Kaduna

Fitaccen malamin nan na Islama kuma babban masani a harkar na'ura mai kwakwalwa, Dakta Isa Ali Pantami yayi tsokaci game da tashin hankalin da aka samu gami da asarar rayuka a garin Kaduna, jihar Kaduna a 'yan kwanakin nan da suka gabata.

Dakta Fantami wanda yayi tsokacin game da lamarin a shafin sa na dandalin sada zumuntar zamani ta Tuwita ya yi tofin Allah-tsige ga wadanda suka tada rikicin tare kuma da yin addu'ar kariyar Ubangiji daga dukkan fitintinu ire-iren su da ka iya tasowa.

Sheikh Isa Ali Pantami yayi magana game da rikicin garin Kaduna
Sheikh Isa Ali Pantami yayi magana game da rikicin garin Kaduna
Asali: Twitter

KU KARANTA: Duk wanda Najeriya ta isa ya iya canza kasa - Buhari

Legit.ng Hausa ta samu cewa da a samu barkewar rikicin kabilanci a garin na kaduna wanda yayi sanadiyyar wata hatsaniya da ta lakume rayuka da dama a garin.

Wannan dai kamar yadda muka samu har sai da ya jaza hukumomin tsaro a jihar suka sanya dokar ta-baci ta hana fita a cikin kokuwar garin kafin a samu a shawo kan matsalar.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya shawarci dukkan wanda yake ganin yana da wata kasar da zai tafi ko kuma kasar ta ishe shi to hanya a bude take don ya fice ya canza kasa.

Shugaban kasar haka zalika ya kara da cewa su da ba suda wata kasa tare da sauran miliyoyin 'yan Najeriya za su zauna nan domin ganin sun gyara kasar tare da maida ta bisa tafarki madaidaici.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng