Ba dole: Duk wanda yaji Najeriya ta ishe shi ya iya canza kasa - Inji Shugaba Buhari
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya shawarci dukkan wanda yake ganin yana da wata kasar da zai tafi ko kuma kasar ta ishe shi to hanya a bude take don ya fice ya canza kasa.
Shugaban kasar haka zalika ya kara da cewa su da ba suda wata kasa tare da sauran miliyoyin 'yan Najeriya za su zauna nan domin ganin sun gyara kasar tare da maida ta bisa tafarki madaidaici.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Yan Boko Haram sun tada gari 2 a Borno
Legit.ng Hausa ta samu cewa Shugaban kasar ya yi wannan maganar ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu jiga-jigan jam'iyyar APC daga jihar Kwara da suka kai masa ziyarar ban girma a karkashin jagorancin Ministan yada Labarai, Lai Mohammed.
Daga karshe kuma shugaban kasar ya shawarci dukkan 'yan Najeriya da suke son ganin kasar ta gyaru da su cigaba da taya shi da addu'a tare kuma da fara canza kan su.
Su ma da suke maida jawabi, sun bayyana cikakken goyon bayan su ga shugaban kasar a zaben da za'a gudanar a 2019.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng