Allahu Akbar! Abubuwa 5 da yakamata ku sani game da marigari Jostis Kutigi

Allahu Akbar! Abubuwa 5 da yakamata ku sani game da marigari Jostis Kutigi

Tabbas duk mai rai mamaci ne a kwana-a tashi watan wata rana inda da rai to tabbas wata rana za'a zamo gawa.

A yau ne dai aka wayi gari da labarin rasuwar tsohon Alkalin Alkalai na tarayyar Najeriya, watau Jostis Idris Legbo Kutigi.

Allahu Akbar! Abubuwa 5 da yakamata ku sani game da marigari Jostis Kutigi
Allahu Akbar! Abubuwa 5 da yakamata ku sani game da marigari Jostis Kutigi
Asali: UGC

KU KARANTA: Wasu jiga-jigan APC na kitsa tsige gwamnan Legas

Bayaga dai wannan mukamin da ya taba rikewa a lokacin rayuwar sa, al'umma da dama ba su san labarin sa ba sosai.

Legit.ng Hausa ta tattaro maku wasu daga cikin abubuwa 5 game da rayuwar tasa:

1. An haife shi ne a 31 ga watan Disemba, shekarar 1939 a garin Kutigi, karamar hukumar Lavun, jihar Neja.

2. Yayi makarantar sa ta Furamare a a garin Lavun kafin daga bisani ya tafi Kwalejin Barewa da kuma Jami'ar Ahmadu Bello, a garin Zariya.

3. Marigayin yayi karatuttuka da kwasakwasai da dama a kasar Ingila, birnin Landan.

4. Ya rike mukamin kwamishinan Shari'a kuma Antoni Janar na jihar Neja har zuwa shekrar 1976.

5. Ya rike mukamin Alkalin Alkalai na Najeriya tun daga shekarar 2007.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel