Bursunoni 35 daga gidan yarin Jos zasu zana jarabawar NECO a 2018
- Hukumar kula da gidajen yari ta kasa NPS, ta ce akalla bursunoni 35 ne daga gidan yari na Jos, za su zana jarabawar NECO a 2018
- Ayedoo ya ce bursunonin da suka hada da maza 32 da kuma mata 3, kuma sun samu horo na musamman don zana jarabawar
- A cewar sa, asusun horarwa na masana'antu ITF ne ya biya kudin jarabawar bursunonin, a cikin bukin cikar asusun shekaru 47 da kafuwa
Hukumar kula da gidajen yari ta kasa NPS, ta ce akalla bursunoni 35 ne daga gidan yari na Jos, za su zauna don zana jarabawar kammala babbar makarantar sakandire, wato NECO a zangon jarabawar na watan Nuwamba/Disamba 2018.
SP Luka Ayedoo, jami'in hulda da jama'a na hukumar, reshen jihar Filato, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Lahadi, a garin Jos, babban birnin jihar.
Ayedoo ya ce bursunonin da suka hada da maza 32 da kuma mata 3, sun samu horo na musamman don zana jarabawar, musamman a bangaren darussan kimiyya da kasuwanci.
KARANTA WANNAN: Ku ji tsoron mu'amala da 'yan matan Agatu - Mrs Comfort ta gargadi jami'an NAF

Asali: Twitter
A cewar sa, asusun horarwa na masana'antu ITF ne ya biya kudin jarabawar bursunonin, a cikin bukin cikar asusun shekaru 47 da kafuwa.
"Wannan jarabawar na daya daga cikin manyan shirye shiryen da ake kanki, na bunkasa rayuwar bursunonin, idan sun koma cikin jama'a, bayan an sallamesu," a cewar Ayedoo.
Jami'innhulda da jama'ar ya bayyana cewa hukumar na kan tattara dukkanin abubuwanda ake bukata don ganin an samu hadin guiwa wajen ilimantar da bursunoni da kuma horas da su sana'o'in dogaro da kai.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng