Ku ji tsoron mu'amala da 'yan matan Agatu - Mrs Comfort ta gargadi jami'an NAF
- Mrs Comfort Alhassan, ta shawarci jami'an rundunar sojin sama NAF da aka tura karamar hukumar Agatu, da su guji yin cudanya da 'yan matan garin
- Air Marshal, Sadique Abubakar ne ya kaddamar da cibiyar karbar koken gaggawar, mai dauke da jami'an rundunar 21 don dakile ta'addanci a yankin
- Ta kuma yi alkawarin tallafawa sojojin tabangaren abincin su, tana mai cewa, "duk abubuwan da suke bukata, kawai su tambaya."
Mrs Comfort Alhassan, shugabar karamar hukumar Agatu, ta shawarci jami'an rundunar sojin sama NAF da aka tura karamar hukumar don gudanar da shirin karbar koken gaggawa, da su kauracewa yin cudanya da 'yan matan garin don kaucewa fushin Ubangiji dana magabata.
A ranar Juma'a a cikin garin Agatu, Alhassan ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a taron kaddamar da cibiyar karbar koken gaggawa da rundunar ta samar a garin na Agatu, cewar ya zamarwa jami'an sojin wajibi su guji yin zinace zinace da matan garin, ko kuma su jefa kawunansu a cikin mummunan yanayi.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal, Sadique Abubakar ne ya kaddamar da cibiyar karbar koken gaggawar, mai dauke da jami'an rundunar 21 don dakile ta'addanci a yankin.
KARANTA WANNAN: An damke wasu mutane 22 da ke da hannu cikin rikicin Kasuwar Magani

Asali: Facebook
A shekara ta 2016, kamfanin labaran ya ruwaito cewa, makiyaya sun kai farmaki a karamar hukumar, wanda ya tilasta mutanen gari guduwa don tsira da rayukansu, yayin da su kuma makiyayan suka kona gidaje da dama a garin.
Shugabar karamar hukumar, ta ce wannan shawarar ta zama dole, sanin cewa "jiki da jini, amma dai ina shawartarsu, da kada su bar sha'awarsu ta rudesu, idan har sunga mace suna sonta to su sanar da iyayenta, amma kada su ce zasu yi zina da ita."
Sai dai, ta jinjinawa gwamnatin tarayya bisa wannan kokari na samar da cibiyar karbar koken gaggawa karkashin rundunar sojin sama a karamar hukumar, tana mai cewa "a yanzu zamu iya yin bacci idanuwanmu rufe".
Ta kuma yi alkawarin tallafawa sojojin tabangaren abincin su, tana mai cewa, "duk abubuwan da suke bukata, kawai su tambaya."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng