Sojojin Najeriya sun bayar da karin sabbin bayanai game da neman Janar Idris Alkali da suke kan yi

Sojojin Najeriya sun bayar da karin sabbin bayanai game da neman Janar Idris Alkali da suke kan yi

A ranar Laraba ne dai dakarun jami'an rundunar sojin Najeriya dake kan aikin neman Janar Idris Alkali da ya bace watan jiya suka gabatar da wasu mutane 13 da suke kyautata zaton suna da hannu a wajen batan na Janar din ga manema labarai a garin Jos.

Birgediya Janar Umar Muhammed dake zaman babban kwamandan rundunar sojin ta 3 dake a Rukuba kusa da garin na Jos ya shaidawa manema labarai cewa za su mika wadanda suka kama din ne zuwa ga jami'an 'yan sanda domin gudanar da cikakken bincike kan su.

Sojojin Najeriya sun bayar da karin sabbin bayanai game da neman Janar Idris Alkali da suke kan yi
Sojojin Najeriya sun bayar da karin sabbin bayanai game da neman Janar Idris Alkali da suke kan yi
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Akwai yiwuwar mai ya koma N205

Kwamandan ya kuma kara da cewa sun kama mutanen ne a kusa da inda aka tsinci motar kuma bayan 'yan tambayoyi suka fahimci cewa watakila mutanen suna da hannun kuma suna da bayanan da za su iya bayarwa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ne Hedikwatar rundunar sojin dake a Abuja ta nada wata runduna ta musamman da aka dorawa ahakin nemo Janar din da ya bata akan hanyar sa ta zuwa Bauchi daga Abuja.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Kano sun aike da takardar sammaci suna gayyatar dan takarar kujerar gwamnan Kano, Alhaji Sagir Abdullahi Takai bisa mutuwar wani tsoho mai shekaru 70 a duniya lokacin da ya ke gudanar da gangami.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan SP Magaji Majiya ya bayyana cewa suna sa ran dan takarar zai mika kansa ga kwamishin 'yan sandan jihar don girmama gayyatar da suka yi masa da kuma ansa wasu 'yan tambayoyi a ranar Litinin mai zuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng