An kama mai kamawa: An kama Yansandan da suka bindige wata budurwa a Abuja

An kama mai kamawa: An kama Yansandan da suka bindige wata budurwa a Abuja

Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da kama wasu jami’anta da bata bayyana adadinsu ba, wadanda take zarginsu da hannu cikin halaka wat budurwa a Abuja, Anita Akpason jim kadan da dawowarta daga kasar Ingila, inji rahoton jaridar Sahara.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a daren Asabar, 13 ga watan Oktoba ne wasu yansanda suka dirka ma Anita harsashi a unguwar Katampe dake babban birnin tarayya Abuja, inda nan take ta fadi matacciya.

KU KARANTA: Rikicin Filato: Gwamnati ta dauki sabbin jami’an leken asiri 350

An kama mai kamawa: An kama Yansandan da suka bindige wata budurwa a Abuja
Anita
Asali: Twitter

Sai dai a ranar Litinin, sai aka jiyo kaakakin rundunar Yansandan Najeriya, DCP Jimoh Ibrahi yana Karin haske game da kisan budurwa Anita, inda yace babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris ya bada umarnin kaddamar da binciken kwakwaf akan lamarin.

“Babban sufetan Yansandan Najeriya, ya umarci kwamishinan Yansandan Abuja da ya kama dukkanin Yansandan dake da hannu cikin kisan, sa’annan ya gudanar da cikakken bincike game da lamarin, tare da tabbatar da hukuncin da ya kamata ya hau kansu.

“Babban sufetan Yansandan yana jajanta ma iyalan Anita, sa’annan ya basu tabbacin za’a bi ma diyarsu hakkinta, a yanzu haka kwamishinan Yansandan jahar ya fara tattaunawa da iyalan marigayiyar, kuma tuni an kama yansandan dake da hannu a cikin bahallatsar.” Inji shi.

Daga karshe Kaakaki Jimoh yace za’a sanar da jama’a sakamakon binciken da zarar an kammala gudanar da shi.

A wani labarin kuma, dakarun Sojin Najeriya sun samu galaba akan wasu gungun yan bindiga dake dajin karmuku a cikin karamar hukumar Birnin Gwari ta jahar Kaduna, inda suka kashe yan bindiga da dama tare da kwace makamansu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel