Allah-daya-gari-ban-ban: Labarin wata tsaliliyar budurwa da ta auri kanta

Allah-daya-gari-ban-ban: Labarin wata tsaliliyar budurwa da ta auri kanta

Wata tsaliliyar budurwa mai suna Lulu Jemimah mai shekaru 32 a duniya da kuma take 'yar asalin kasar Uganda ta jefa al'ummar Nahiyar Afrika da ma duniya baki daya cikin al'ajabi bayan da ta auri kanta.

Budurwar dai kamar yadda muka samu ta yanke shawarar ta auri kanta ne biyo bayan matsin lamba da ta fuskanta daga iyayen ta wadanda suka ce lallai dole ne ta fito da miji tayi aure.

Allah-daya-gari-ban-ban: Labarin wata tsaliliyar budurwa da ta auri kanta

Allah-daya-gari-ban-ban: Labarin wata tsaliliyar budurwa da ta auri kanta
Source: Twitter

KU KARANTA: Kayatattun hotunan bikin Ado Gwanja

Legit.ng ta samu cewa sai dai a maimakon ta fitar da miji, Lulu Jemimah sai ta shirya kasaitaccen bikin aure a garin na su inda kuma ta sanar da cewa ita yanzu ta yanke shawarar ta auri kanta kawai.

Lamarin dai ya dauki hankali sosai inda ta bayyana cewa ita yanzu ba namiji ne a gaban ta ba domin karatu ta sa a gaba tana kuma so ta kammala karatun ta na digiri na biyu da take yi a jami'ar Oxford, kasar Ingila.

Allah-daya-gari-ban-ban: Labarin wata tsaliliyar budurwa da ta auri kanta

Allah-daya-gari-ban-ban: Labarin wata tsaliliyar budurwa da ta auri kanta
Source: Twitter

Sai dai kuma wani lamarin da ya zo a ba zata shi ne yadda dukkan dangin ta babu wanda ya halarci bikin nata wanda hakan ke nuna rashin amincewar su da goyon bayan su kuma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel