2019: Mayakan Neja Delta sun ce shugaba Buhari ya zarce kawai!

2019: Mayakan Neja Delta sun ce shugaba Buhari ya zarce kawai!

- An zabga ayyuka a Neja Delta

- Sun tuba sun daina fasa bututan mai

- An sami masoya Buhari a yankin Igbo da Ijaw

2019: Mayakan Neja Delta sun ce shugaba Buhari ya zarce kawai!
2019: Mayakan Neja Delta sun ce shugaba Buhari ya zarce kawai!
Asali: Depositphotos

A bayan da ya kayar da Goodluck Jonathan, a 2015, shugaba Muhammadu Buhari ya fuskanci masu tada qayar baya a yankin Neja Delta mai arzikin ma fetur, inda suka sha alwashin baza su bari kasar nan ta mori mai ba dagayankin.

Sai dai bayan da Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara qauyukansu lokacin yana mukaddashin shugaban kasa, ya roki sarakunansu dasu tsawatar musu su yi hakuri su bari su gani ko gwamnati zata tuna dasu.

A yanzu, mayakan yankunan sun ce sun gani a kasa, sun kuma bari a fidda mai daga yankin, kuma suna fata ma shugaba Muhammadu Buharin ya zarce a badi.

DUBA WANNAN: Tun 2015 nake munafuntar Goodluck Jonathan - Akpabio

Sun canza sunansu a baya, daga Avengers of the Niger Delta zuwa Reformed Niger Delta Avengers, wanda ke nuna sunn tuba sun bi.

An saka su cikin wadanda shugaba 'Yaraduwa yayi ma afuwa a 2008, inda ake biyansu makudan albashi, da ma kaisu karatu kasashen waje.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel