Asiri ya Tonu: Yadda Birgediya Janar Apere ya tura sojoji aka kashe su da gan-gan
- Wani soja ya bankado badakalar da ake yi a cikin rundunar sojin Nigeria
- Jawabin ya bayyana Birgediya Janar, Clement Apere a matsayin wanda ke tura soji ana kashe su
- Tsoron ankwar da akeyiwa sojoji barazana da ita ya sa kowa yayi shiru akan cin kashin da akewa sojoji a yankin Arewa maso Gabas
An bayyana Birgediya Janar, Clement Apere wanda ya ke a runduna ta 707 dake a Makurdi, a matsayin wanda ke sayarwa mayakan Boko Haram makamai, sannan daga bisani ya tura sojoji yaki, wanda hakan ya baiwa Boko Haram damar tarwatsa sojoji 800 da kashe daruruwa daga ciki.
Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da wani soja ya rubuta, kana kungiyar CUPS karkashin Dr. Idris Ahmed ta wallafa a kafafen sada zumunta na zamani, a ranar 23 ga watan Augusta, 2018.
Jawabin ya ce "An baiwa Birgediya Apere, wanda ya canja suna zuwa Texas Chuckwi, kuma sabon kwamandan runduna ta 7, makudan kudade don ya horas da sojoji 150 da ya kira Rundunar soji ta musamman, a kasar waje.
"Sai dai sam bai horas da su ba, basu da wani ilimi na yaki, kawai ya dauki makamai ya basu tare da bakaken kaya, tare da yi musu karyar su sojojine na musamman. Sai gashi kwanaki hudu da suka wuce, ya tura su garin Garshiga a Maiduguri, inda aka kashesu gaba daya.
"Amma abin mamaki shine, rundunar soji ta kasa ta musanya kisan wadannan sojoji 150. Tana mai ikirarin cewa bata da wata masaniya na rashin dawowar wannan tawaga garin Maiduguri, saboda sun bar sansaninsu ne a ranar daya ga watan Yuli, 2018.
KARANTA WANNAN: Hajjin bana: An kama wani dan arewacin Najeriya a Saudiyya saboda dukan dan sanda
"Idan aka koma barikin rundunar soji ta musamman da ke garin Azare, jihar Bauchi, a nan ne ake daukar soja ba abakin komai ba, sama da sojoji 15 ke kwana a daki daya, wasu ma a majami'u da masallatai suke kwana.
"Amma wai a hakan ne za'a ce ana bincike kan manyan jami'an soji dake yin almundahana, bayan an san su, an kuma san inda suke. Kawai dai wasu mutane sun fi karfin hukuma, kamar dai janar janar dake zaune a Maiduguri, dama arewa maso gabashin kasar.
"Idan har ana neman gaskiya ne, to a tambayi mutanen Maiduguri, ko a je sansanin soji na musamman da ke Kashua Fara da kuma Low cost. Sojoji sun gaji da wannan cin kashin, kawai dai basu da kwarin guiwar amayar da abinda ke ransu.
"Kowane soja na tsoron ankwar da kullum ake masu barazana da ita, an mayar da sojin Nigeria tamkar bayi, yayin da aikin soji ya zama kamar wata kasuwa da ke samar da Miliyoyin kudade ga manyan sojin kasar." A cewar jawabin sojan.
Daga karshe Dr. Idris ya rufe jawabin nasa da wani sako a madadin CUPS, in da sakon ya ce:
"Ya ku 'yan Nigeria, kungiyar CUPS na aiki kusan awa 24 a kowace rana tare da wannan jarumin sojan da ya fallasa abubuwan da ke faruwa, in da kuma ana kan tattara bayanai don gurfanar da Birgediya Janar Clement Apere a gaban kotu.
Muna rokon Allah ya kare 'yan Nigeria dama kasar baki daya. Amin".
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng