Da dumin sa: Mummunan hatsarin mota ya rutsa da dan majalisa daga jihar Filato

Da dumin sa: Mummunan hatsarin mota ya rutsa da dan majalisa daga jihar Filato

Mummunan hatsarin mota ya rutsa da tsohon mataimakin kakakin majalisar jihar Filato dake a yankin Arewa ta tsakiya mai suna Yusuf Gagdi a ranar Asabar din da ta gabata.

Kamar dai yadda muka samu, hatsarin ya auku ne lokacin da motar da ke dauke da dan majalisar tayi taho-mu-gaba da wata motar dauke da wabi babban jami'in rundunar sojin saman Najeriya.

Da dumin sa: Mummunan hatsarin mota ya rutsa da dan majalisa daga jihar Filato

Da dumin sa: Mummunan hatsarin mota ya rutsa da dan majalisa daga jihar Filato

KU KARANTA: Ku zo ku ga sarkin da yace yafi Dangote kudi a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4 na marece jiya din kuma shi jami'in sojin saman Najeriya yanzu haka ma yana asibiti yana karbar kulawar likita.

A wani labarin kuma, Rundunar dakarun sojin Najeriya dake sintirin tabbatar da tsaro da samar da zaman lafiya a jahohin Arewa ta tsakiya a ranar Asabar din da ta gabata sun sanar da yin kicibis da wasu 'yan bindiga a karamar hukumar Guma ta jihar Benue.

Sanarwar afkuwar hakan dai ta fito ne dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na hedikwatar rundunar dake Abuja, Texas Chuku inda yace kuma dakarun nasu sun yi dauki ba dadi da 'yan bindigar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel