Da dumin sa: Hatsarin mota ya rusta da Hororabul Ado Doguwa, dan majalisar wakillai daga Kano
Labarin da muke samu daga majiyar mu ta Rariya na nuni ne da cewa Honarabul Alasan Ado Doguwa, dan majalisa ne mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada a jihar Kano ya tsallake rijiya da baya biyo bayan wani hatsarin mota da ya rutsa da shi.
Kamar yadda muka samu, hatsarin dai ya same shi ne tare da abokan tafiyar sa akan hanyar sa daga Kano zuwa Abuja amma dai ba'a samu rasa rayuka ba.
KU KARANTA: Sabon rikici ya barke a jihar Filato, mutum 3 sun rasu
A jiya ne dai muka kawo maku labarin cewa Honorabul Alhassan Ado-Doguwa yace dukkan wadanda suka canza shekar suka koma PDP daga APC tamkar sun kashe kan su ne sun binne da kansu.
A wani labarin kuma, A halin da ake ciki yanzu haka dai garin Sokoto ya dauki harami inda kusan duk inda mutum ya kalla zai ga kowa na ta shire-shiren tarbar tsohon gwamnan jihar Alu Magatakarda Wamakko da sauran jiga-jigan APC a jihar da za su zo yin gangami.
Wannan dai kamar yadda muka samu, yana zuwa ne kwanaki kadan biyo bayan ficewar gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal daga jam'iyyar APC zuwa PDP a jihar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng